Ka kaddamar da makiyayan Fulani a matsayin yan ta’adda – Hon Gyang ya roki Buhari
- Hon Gyang ya roki shugaba Buhari ya kaddamar da makiyayan fulani a matsayin yan ta'aada
- Gyan ya ce yakamata gwamnatin tarayya ta dauki al'amarin makiyaya Fulani kamar yan yadda ta dauki kungiyar Boko Haram
Wani dan majalissar wakilai daga jihar Filato Istifanus Gyang bukaci gwamnati shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kaddamar da makiyayan Fulani a matsayin yan ta’ada.
A jawabin da yayi, ya ce ya kamata gwamnati ta dauki al’amarin makiyayan Fulani kamar yadda ta dauki al’amarin kungiyar Boko Haram.
Gyang yayi wannan jawabin ne a Abuja a lokacin da yake mayar da martani ga nasihar da kungiyar Matasan jihar Filato (PPYM) suka yi masa na cewa, lokaci yayi da yakamata yayi aikin da suka tura shi majalissa, bawai ya rika siyayasa da rayuwar mutanen mazabar sa.
KU KARANTA : Yansada sun kama dalibai 7 da laifin kashe abokin su da suke zargin sa da zama dan luwadi a jihar Kano
Gyang yayi tir da rikicin da ya barke tsakanin jami’an tsaro da mutanen karamar hukumar Riyom.
Dan majalissar ya zargi sojoji da cin zarafin mutanen mazabar sa da kuma aikata laifin fyade.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng