Matan kasuwar Sapele sun yi tattaki da sanduna zuwa karamar hukumar su don an kwace musu dubu arba'in-arba'in
- Sun karbi kudin su sannan suka sa aka fatattake su
- Sun ce ko a biya su kudin su ko a yi ta ta kare
- Shugaban kwamitin kasuwar yana hango su ya ranta a na kare
A jiya matan babbar kasuwar Sapele suka yi tattaki zuwa karamar hukumar su don su nuna fushin su saboda kwamitin kasuwar na cin zarafin su.
An samu labarin cewa shugaban kwamitin, Mista Perkins Umukoro, tuni ya tsere da ya hango gungumin matan sun durfafi inda yake saboda tsoron kar suyi masa wal-mukalifatu.
Shuwagabannin matan kasuwar sun ce kwamitin ya tilasta musu biyan dubu arba'in-arba'in kafin a bar su iya ci gaba da kasuwancin su a sabon sashin kasuwar da aka gina mai daukar shaguna 1,532.
Ko da suka gama biyan kudaden, sai kwamitin suka zo da 'yan banga suka fatattake su a kan cewa ba su da ikon yi kasuwancin su a bakin wajen.
Wata shugaba a cikin su, Misis Aminoma McGrey, ta ce, "Don me za su shuna mana 'yan daba? Don me za su kore mu bayan mun biya kudi? In so suke mu tashi sai su fara dawo mana da kudaden mu, sannan a fara maganar tashi. Amma daga cin kudin mu sai a shuno mana 'yan daba su fatattake mu?"
A tattakin da suka yi sun dauki sanduna da filanki-iflanki masu dauke da rubutuce-rubucen fushi: "Ba zamu yadda ba! Ba za mu yadda ba! Ko a biya mu kudin mu, ko ta ayi ta ta kare!" da sauransu.
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Majalisar dattijai ta amince da cin bashin $5.5bn da Buhari zai yi
Manema labarai sun nemi su ji ta bakin shugaban kwamiti Perkins amma tun da ya tsere ba a kara jin duriyar sa ba. Amma wani dan kwamitin, Mista Christmas Godwin, ya fito ya basu hakuri ya ce za su duba hakan. Ya kwantar musu da hankali.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:
labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng