Dan Boko Haram ya yi wa mahaifin sa yankan Rago a Yobe

Dan Boko Haram ya yi wa mahaifin sa yankan Rago a Yobe

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar ta Yobe, DSP Zubairu Jafiya, ya tabbatar da faruwar hakan, ya shaidawa manema labarai cewar wasu 'yan ta'adda mutum hudu suka aiwatar da kisan.

Ya kara da cewar "sun yi harbin iska tare da tsorata mazauna kauyen kafin daga bisani su kashe wani mai suna Alhaji Kwaramtcheri".

Dan Boko Haram ya yi wa mahaifin sa yankan Rago a Yobe
Dan Boko Haram ya yi wa mahaifin sa yankan Rago a Yobe

Kakakin ya bayyana cewar bayanan kisan sun yi karanci sannan ya zuwa yanzu basu kama kowa dangane da aikata laifin kisan ba.

DUBA WANNAN: Kada ka samu damuwa, saura kiris kaji a-lat - Adeosun ta tabbatarwa wanda ya yi fallashen kudin Ikoyi

Wani mayakin kungiyar Boko Haram ya yanka mahaifin sa ranar litinin a kauyen Muktum dake yankin karamar hukumar Gujba a Jihar Yobe.

Dan Boko Haram din ya yanka mahaifin na sa, Malum Kwaramtcheri, a jiya litinin bayan da ya lallaba ya shiga kauyen tare da wasu abokan sa guda 4 da misalin karfe 11 na dare.

Wani mazaunin kauyen, Usman Kura, ya shaidawa manema labarai cewar mahaifin dan Boko Haram din tsohon kansila ne kuma fitaccen dan siyasa a garin Ngirbuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng