Yadda luwadi ya jefa wani tsoho dan shekara 65 cikin bala'i da kaskancin rayuwa
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Neja dake a arewa ta tsakiyar Najeriya ta cafke wani tsohon banza dan shekara 65 mai suna Patrick Kalu bisa ga laifin yin luwadi da yaro dan shekara 15 a duniya mai suna Victo Inne a kauyen Karimo a cikin satin da ya gabata.
Jami'an yan sandan dai sun kama ne turmi da tabarya yayin da yake lalata da yaron a kauyen da rana tsaka gatse-gatse kamar dai yadda majiyar mu ta Northern City News ta labarto mana.
KU KARANTA: Sace-sacen rashin kunya na rugawa a mulki na - Buhari
Legit.ng dai har ila yau ta samu cewa tsohon ya shaidawa manema labarai cewar ya shafe akalla shekaru biyu kenan yana yin wannan danyen aikin tun bayan da ya bar iyalin sa a jihar Abia ya taho jihar Neja ya kuma fara sha'awar yin lalata da yara kanana.
To sai dai kuma tsohon ya karyata zargin cewa wai tsafi ne ya ke sanya shi haka, inda ya bayyana cewa shi sha'wa ce kawai sannan kuma ya bayyana kan sa a matsayin sakarai wanda rayuwar sa ta lalace ya kuma kaskanta a idon duniya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng