Ikon Allah: Kalli hoton wani mutumi da aka haifa da fuskoki guda 2
Allah buwayi, gagari misali, tabbas idan mutum yayi duba ga halittu daban daban da Allah ya halitta, hakan ya ishe shi zama izina muddin yayi tadabburi.
Wani shafin bayar da tarihi a Facebook, mai suna ‘Pictures in History’ sun kawo labarin wani mutumi mai suna Edward Mordrake wanda aka haife da fuskoki guda biyu.
KU KARANTA: Zaɓen 2019: Atiku sai ya nemi gafarar Obasanjo muddin yana son zama shugaban kasa a Najeriya
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an haifi Edward ne a shekarar 1890, inda dayan fuskan daya fito a bayan kansa yana iya dariya da kuka, tare da yin wasu irin koke koke masu ban tsoro, duk ba tare da iya sarrafawar Edward ba.
Sakamakon damuwa da Edward ya shiga saboda wannan fuska nasa, ya taba rokon likitoci da su taimaka masa su cire masa shi, inda ya bayyana fuskar a matsayin ‘fuskar shaidan.’, sai dai ba’a samu likitan da yayi karanmabin yin hakan ba.
Bayan gajiya da halin da yake ciki ne, sai Edward ya hallaka kansa a shekarar 1913, yana mai shekaru 23.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng