"Tsigar Yesu Almasihu karya ne, Kuma ba dan Allah ba ne" - Revaren. Bempah
- Revaren Bempah ya kawo wata sabuwar fahimta a addinin krista
- Bempah ya ce ‘Yeshua HaMashiach’ shine aihin suna Yesu Almasihu (Jesus)
- Addinin krista a yanzu tatsuniya ce da daular Romawa na farko suka hada inji Ravaren Bempah
Wani shahararren malamin addinin krista a kasar Ghana, Ravaren Isaac Owusu Bempah, shugaban cocin Glorious Word Power Ministry International ya kawo wani sabuwar fahimta a addinin krista.
A lokacin da Rev. Bempah yake hira da gidan talabijin din Kofi TV, ya ce Yesu Almasihu ba dan Allah ba ne kuma tsigar ‘Jesus’(Yesu) da ake kiran sa da shi jabu ne ba shi bane ainihin sunan sa.
Bempah yace ainhin suna sa shine ‘Yeshua HaMashiach’ suna ‘Jesus’(YesuAlmasihu) Kage ne.
Raveren Bempha ya ce sunan Yeshua Hamashiach ya na nufin zaben Ubangiji, saboda haka ya na mamakin yadda aka yaudari kristocin duniya aka su, su ka dauki ‘Jesus’ (Yesu) a matsayin dan Allah kuma abun bauta a gare su.
KU KARANTA : Dansanda ya yiwa soja dukan tsiya a wajen na’urar ATM dake Damaturu
Bempha yace tarihin Yesu Almasihu da muka karanta a takardun tarihi, da kuma sabuwar Injila tatsuniya ce da Daular Romawa na zamanin farko suka hada kuma suka mayar da shi addinin krista.
Duk lokacin da wani abun al’ajabi ya faru bayan Fastoci sun kira sunan ‘Jesus’ (Yesu Almasihu), ba sunan sa bane ke aiki ruhin Yeshua HaMashiach ke aiki saboda shine sanannen suna a samaniya, kuma dole masu imani dake duniya su yarda da wannan suna.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook : https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter : https://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA : Sabuwar manhajar labarai na Legit.ng
Asali: Legit.ng