Asaba: Wata sabuwar rikici na kokarin kunno kai tsakanin Hausawa da gwamnatin Delta
- Ana shirin rushe gidajen al’ummar Hausawa a Asaba don gina wata sabuwar birni
- Gwamnatin jihar Delta ta bukaci Hausawa mazauna yankin Cable Point a Asaba su kaura daga yankin
- Al’ummar sun yi alkawalin yin tsayayya da duk wani ƙoƙari na tilasta su daga yankin
Akwai kishin-kishin tashin hankali a garin Asaba bayan abin da mazaunar garin suka bayyana a matsayin shirin fitar da su daga yankin wanda suka ce sun zauna a ciki tun shekaru 200 da suka gabata.
Wannan lamarin ta biyo bayan tsare-tsaren da gwamnatin jihar Delta ta yi tare da wani kamfani mai zaman kanta, Rexwood Nigeria Limited, don sake mayar da yankin zuwa wata sabuwar birni wanda zai hada da wuraren shagali da wasanni, hotels, shagunan kasuwanci, gine-gine da wuraren zama a cikin abin da aka kira "New Dubai".
Al’ummar yankin sun bayyana cewa wani Mista Ubaka J. Ubaka ya sadu da su kimanin watanni uku da suka inda ya gabatar masu da takadar tsari wanda ta bukaci su kaura daga yankin don gina sabuwar birnin watau “New Dubai”. Mutanen sun ki amince da shirin gwamnatin saboda bai samar da wani kyakkyawan shiri nan gaba ba.
"Mun zauna a nan shekaru fiye da 200. An haife ni a nan. An haifi mahaifina a nan kuma an haifi kakana a nan. Sun zo kasuwanci kuma sun zauna a nan kuma wannan gida ce a gare mu. Muna taimaka wa tattalin arzikin wannan wurin; muna da kasuwanni da yawa a nan kuma muna kasuwanci masu halalci. Kaburburan kakanninmu suna nan kuma yanzu suna neman mu bar gidajenmu", in ji Sarkin Hausawa na Asaba, Alhaji Ibrahim Baba Gero.
KU KARANTA: Markafi yayi magana akan abun da zai faru a ranar babban taron jam'iyyar PDP
Cable Point wani yanki ne da ke yankin garin Asaba tare da fiye da gidaje 2000 da shaguna. Al’ummar Hausa sun ce suna da kimanin gidajen ibada 20 a cikin yanki da shaguna da wuraren kasuwanci.
A cikin makon da ya wuce, tashin hankali ta kunno kai a lokacin da wasu jami’an gwamnati suka zo yankin suka fara rubuce-rubuce a gidac. Al'umma sun taru suka kori su.
Sarkin Hausawa ya shaida wa majiyar Legit.ng a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba cewa, babban darakta na hukumar bunkasa harkokin gida na jihar Delta (DSCTDA), Cif Clement Ofuani ya gaya musu cewa za a fitar da su daga yankin don samun damar aiwatar aikin.
KU KARANTA: Zaben Anambara : Ohanaeze ta mayar wa kungiyar IPOB martani akan hana mutanen Anambara fito wa yin zabe
"Ya ce dole ne mu bar yanki", in ji Baba Gero.
Wannan lamarin yasa al'ummar suka yi kira ga hukumar 'yan sanda da kungiyar gwamnonin arewa da babban daraktan ‘yan sandan farar hula da sarkin Kano da na Zazzau da sauransu a wata wasika ta ranar 9 ga watan Nuwamba, 2017.
Mazauna sun yi alkawalin yin tsayayya da duk wani ƙoƙari na tilasta su daga yankin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng