Wasanni: Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana farashin dan wasa Gareth Bale
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana farashin dan wasan ta Gareth Bale ga kungiyoyi masu sha'awar siyan dan wasan na ta.
Kungiyar ta Real Madrid ta bayar da farashin Fan Miliyan 85 kamar yadda jaridar Daily Mirror ta ruwaito, inda kungiyoyi da dama musamman kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fi kowace kungiya zakewa wajen sha'awar mallakar dan wasan dake taka leda a kasar Andalus.
Dan wasan na kasar Wales ya shafa fama da jinya ta raunuka daban-daban a yayin da yake kungiyar ta Real Madrid, wanda yanzu haka hukumomin kungiyar suke ganin ya kamata su sayar da shi tun kafin darajar sa ta far raguwa.
KARANTA KUMA: Ku biya malamai basussukan su ko mu rufe makarantu - Kungiyar Malamai ga Gwamnoni
Dan wasan mai shekaru 28 wata babbar kadara ce ga babbar kungiyar tamola ta Real Madrid, sai dai kash ciwon kunkuru da cinya sun matsa masa, wanda ya shafe tsawon lokuta da baya motsawa a harkar wasannin kungiyar.
Legit.ng ta fahimci cewa, akwai tsohuwar kungiyar kwallon kafa da Bale ya takawa leda ta Tottenham dake sha'awar mallakar dan wasan, sai kuma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ita ma ta nuna irin ta ta sha'awar akan dan wasan.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng