Dalilin da yasa Alex Iwobi ya zabi bugawa Najeriya kwallon kafa - Wenger

Dalilin da yasa Alex Iwobi ya zabi bugawa Najeriya kwallon kafa - Wenger

- Ingila ta ja kafar kiran shi don ya buga mata wasa

- A da ya bugawa Ingila da Najeriya wasa

- Iwobi zai bugawa Najeriya a gasar wasan kwallon kafa ta duniya

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, ya bayyana dalilin da ya sa dan wasan shi Alex Iwobi ya zabi buga wa Najeriya kwallon kafa a maimakon Ingila. Ya ce jan kafar da Ingila ke yi ne ya sa ya dau wannan matakin.

Dalilin da yasa Alex Iwobi ya zabi bugawa Najeriya kwallon kafa - Wenger
Dalilin da yasa Alex Iwobi ya zabi bugawa Najeriya kwallon kafa - Wenger

"Alex Iwobi ya bugawa kungiyar Najeriya da Ingila a da, amma kasar Ingila sun ja kafa wajen kiran shi don ya buga musu a gasar wasa ta kwallon kafa ta duniya (World Cup) da za'a yi a badi." Inji Wenger.

Alex Iwobi, dan wasan gaba a kungiyar Arsenal, yana da zabi ya taka leda ga kasar Ingila amma saboda jan kafar da suka yi wajen kiran dan wasan zuwa kungiyar kwallon kafa ta kasar sai ya zabi taka leda tare da kasar sa ta haihuwa Najeriya.

DUBA WANNAN: 'Yan mata 26 daga Najeriya masu kokarin zuwa Turai ne suka nutse suka mutu a tekun bahar Rom

Iwobi dai yana da alaka ta jini da tsohon gwarzon dan wasan Najeriya, Austin Jay Jay Okocha, kuma kusan dan wasa Iwobi na kwaikwayon salon wasan kawun sa, Okocha.

Zabin Iwobi na bugawa kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ya zamar wa kasar karin armashi musamma irin rawar da ya taka wajen fitowar Najeriya cikin sahun kasashen da fafata a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a buga a kasar Rasha shekara mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng