Al’umma daga ciki da wajen jihar Gombe sun halarci jana’izar marigayiya Hajiya Yalwa Goje
Dubun dubatan masoya, yan uwa, abokan arziki da ma magoya baya ne suka halarci jana’aizar marigayiya, uwargidar tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje.
A satin data gabata ne dai, Hajiya Yalwa Goje ta rasu a kasar Amurka, bayan tayi fama da rashin lafiya, inda ta mutu ta bar yaya, jikoki, iyaye da kuma mijinta.
KU KARANTA: Cin amana ruwa ruwa: Wasu ƙatta ƙattan samari guda 2 sun zakke ma yar maƙwabcinsu
Cikin wadanda suka halarci jana’izar sun hada da shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo, da sauran manyan mutane.
Shima a nasa bangaren, shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya aika ma Sanata Goje takardar ta’aziyya, inda yake jajanta masa sakamakon rashin da yayi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Cikin tawagar da suka wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin jana’izar sun hada da ministan Ilimi, Adamu Adamu, Ministan Abuja, Muhammad Musa Bello, karamin ministan wuta da ayyuka Hassan Mohammed.
Sauran sun hada da dna uwan shugaban kasa Musa Daura, babban sakataren fadar shugaban kasa Jalal Arabi, hadimin shugaban kasa Sarki Abba da kuma babban akanta na kasa, Ahmad Idris.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng