'Yan mata 26 daga Najeriya masu kokarin zuwa Turai ne suka nutse suka mutu a tekun bahar Rom, kuma an kama wadanda ke da jirgin ruwan
Su dai kasashen Turai wadanda suka san hakkin dan-Adam, sai su fita teku neman wadanda ke gudowa daga Aika saboda su ceto su su kaisu doron kasa, wannan ya sa masu ffito da masu safara ke karbar kudaden mutane su watso su teku su gudu su barsu.
Da yawa daga wadanda ke guduwa daga Najeriya, suna yankawa ta Nijar ne, su shiga sahara, su yi ta bulaguro har Libya, daga nan sai su hau jiragen ruwa su shallaka sai Italiya ko Malta, ko Girka, wasu kuwa Spaniya suke zuwa ta hanyar Morocco, domin su isa ga Turai.
A irin wannan bulaguro dai, kishirwa a yunwa da azabtarwa, da ffashi da makami, da cin zarafi, da fyade, da bautarwa, da kwacen kudade, da ma lumewa aruwa, duk suna cikin hadurra da masu wannan niyya kan fada.
DUBA WANNAN: Dubi ministoci da zasu fi kowa kwasar kudi a kasaffin bana
In kuma sun isa, yawanci babu aikin da suke samu, banda karuwanci, ko kwadago, ko wankau, ko reno, ko wankin mita, wadanda duk iliminka babu yadda zaka yi sai ka ajje ilimin, domin kowa ta kansa yake. Wasu kuwa a titi suke kwana su daskare a lokutan sanyi.
A wannan karon, a makon jiya, 'yan mata 26 ne daga cikin daruruwa, wadanda suka yi wannan fita daga jihar Edo suka nutse a Teku, kuma duk sun hallaka, shekarunsu sun fara daga 14 har zuwa 30, inda wadanda suka sha suka ce rashin aiki da talauci ne ya jefa su wannan tafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Dora Omoruyi, budurwa dalibar jami'a, 'yar shekara 23, tace babu aikin yi shi yasa ta biyo su, ita an ceto ta har ta tsallaka Turai. Ta bayananta kuma an kama wadanda suka amshi kudinsu domin tafiyar, suka kuma bautar da su da yi musu fyade.
Hukumomi sun kama sune Al Mabrouc Wisam Harar, from Libya, and Egyptian Mohamed Ali Al Bouzid, wadanda suka makare jirgin ruwan da kusan mutum 400, da suka ga zai lume kuma, suka dire suka yi iwo, suka tsere suka barsu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng