Ku kalli hotunan irin abincin da ake ba masu tsaron fadar shugaban kasa
Takaici dai ya dabaibaye yan Najeriya da dama yayin da wasu hotunan da aka yi ikirarin cewa na kalar abincin da ake bawa jami'an tsaron dake gadin fadar shugaban kasar Najeriya ne ya bazu a kafafen sadarwar zamani.
Kamar dai yadda majiyar mu ta gidan jaridar Sahara Reporters ta fallasa, ta bayyana cewa duk da irin makudan kudaden da ake warewa da suka kai akalla Naira biliyan 1, sun bayyana kalar abincin a matsayin na cin mutunci kuma kaskanci.
KU KARANTA: Ban taba yin karya ba - Lai Muhammad
Legit.ng dai ta samu cewa a tun farko ma dai shekaranjiya shugaban kasar na Najeriya ya gabatar da kasafin kudin shekara ta 2018 da ya haura Naira Tiriliyan 8 a gaban 'yan majalisar tarayya kamar dai yadda doka ta tanadar.
Ga dai hotunan abincin nan:
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng