Yadda marigayi Murtala Muhammed ya zama shugaban kasa yana ɗan shekara 37

Yadda marigayi Murtala Muhammed ya zama shugaban kasa yana ɗan shekara 37

Kimanin shekaru 78 da suka gabata ne aka haifi tsohon shugaban kasar Najeriya a zamanin mulkin Soja, Marigayi janar Murtala Muhammed, a ranar 8 ga watan Nuwambar 1938 a garin Kano.

Murtala Muhammed wanda shine shugaban kasa na hudu a jerin shuwagabannin Najeriya, ya fito ne daga dangin Gynawa, kuma ya halarci sakandaren Barewa dake Zaria, kamar yadda History Ville ta bayyana a shafin Facebook.

KU KARANTA: Ya tsinci dammin tamanin kuɗi, Naira 582,400 a KEKE NAPEP, ya mayar ma mai su

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Murtala ya shiga aikin Soja a shekarar 1958, inda ya samu horo a kwalejin horas da Sojoji a Teshie, kasar Ghana, inda tsohon shugaban Biyafara Emeka Ojukwu ya koyar da shi.

Yadda marigayi Murtala Muhammed ya zama shugaban kasa yana ɗan shekara 37
Marigayi Murtala

Daga nan sai ya zarce makarantar horas da hafsan Soji, Royal Military Academy Sandhurst dake kasar Ingila, daga bisani aka rantsar da shi a matsayin hafsan Soja a shekarar 1961.

Murtala ya cigaba da samun karin girma, inda ya zama shugaban kasa a shekarar 1975 zuwa 1976, inda aka bindige shi tare da mai tsaronsa yayin dayake kan hanyarsa ta zuwa ofishinsa.

Bayan kashe Murtala, mataimakinsa, Olusegun Obasanjo ya dare madafan mulki, sa’annan ya kama wadanda suka kashe Murtala a karkashin jagorancin Kanal Buka Suka Dimka, kuma aka kashe su.

A kokarinta na tunawa da Murtala Mohammed, gwamnatocin da suka biyo baya sun sanya hotonsa akan kudin Najeriya, naira 20, sa’annan an sanya ma filin sauka da tashin jiragen sama na jihar Legas, sunan Murtala.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng