An garkame shugaban kasar Yemen a wani gida a kasar Saudiyya
- Kasar Saudiyya ta garkame shugaban kasar Yemen da wasu mukarrabansa
- Har a yanzu dakarun Saudiyya da na UAE suna cikin Yemen suna gumurzu
- Tun a farkon shekarar nan Shugaba Hadi ke kokarin komawa gida Yemen
Kasar Saudiyya ta garkame shugaban kasar Yemen tare da ‘ya’yansa, da wasu mukarrabansa sama da tsawon wasu watanni ta hana su komawa kasar su.
Wannan ya samo asali ne saboda ba’a ga maciji tsakanin shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi da kuma tarayyar kasashen karabawa (UAE), sannan kuma da yakin da Saudiyya ta ke yi da Houthi, ‘yan Shi’ar da suke so su mulke Yemen.
DUBA WANNAN: Dalibai a makarantun Kaduna sun fito zanga-zanga a kan sallamar malaman makaranta da gwamnatin jihar tayi
Wannan yakin an fara shi tun 2015, kuma har a yanzu haka dakarun Saudiyya da na UAE suna cikin Yemen suna gumurzu.
A ‘yan kwanankin nan kungiyar Houthi ta harbawa Saudiyya bam wanda ya tashi a Riyadh. A saboda haka Saudiyya ta kara zafin takunkumin da aka sawa Yemen, wanda ya janyo kudin man su ya tashi har ya kusa ninkawa.
Hadi ya je Saudiyya tun farkon shekaran nan amma tun daga nan Saudiyyya ta hana shi komawa kasar sa. Har filin jirgi ya je zai shiga jirgi ya koma suka tasa keyar sa suka maida shi gida.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng