Cizon kunnen makoci ya yiwa wani mutum sanadin daurin shekara 5 a jihar Osun

Cizon kunnen makoci ya yiwa wani mutum sanadin daurin shekara 5 a jihar Osun

Wata babbar kotun jihar Osun, ta zatar da hukuncin dauri na shekara biyar kan wani Olaniyan Isaah bisa laifin cizon kunnen makocin sa da ya yi.

Olaniyan ya gurfana a gaban Alkali mai shari'a Raheem Siyanbola a ranar 10 ga watan Oktoba na shekarar 2016, inda kotun ta kama shi da laifuka uku wanda ya hadar har da yunkurin kisan kai.

Jami'in dan sanda mai shigar da kara Mista Bamidele Salawu ya shaidawa kotu cewa, wannan laifi ya saba dokar jihar ta Osun karkashin sashe na 320, 335 da kuma 338.

Bamidele ya cigaba da shaidawa kotu cewa, a ranar 7 ga watan Yuli na shekarar 2015, a lamba 1 ta layin Balaji Olufunmi dake unguwar Ipetumodu a jihar Osun, Olaniyan ya ketare iyakar dakin wani Mista Alonge Emmanuel, inda ya haye kansa da wani karfe na rodi sakamakon zargin sa da yake na laifin alaka da uwar gidan sa.

Cizon kunnen makoci ya jefa wani mutum zama a gidan Kaso har tsawon shekara 5 a jihar Osun
Cizon kunnen makoci ya jefa wani mutum zama a gidan Kaso har tsawon shekara 5 a jihar Osun

Legit.ng ta ruwaito daga lauyoyi masu karar wanda ake tuhuma da sanadin jaridar Daily Post cewa, wannan mutanen biyun sun shiga artabu inda Olaniyan ya samu nasarar gutsure kunnen Emmanuel.

KARANTA KUMA: Hanyoyin inganta Lafiya 7 da Namijin Goro ke yi a Jikin dan Adam

Emmanuel bai yi wata-wata ba sai ya garzaya ofishin 'yan sanda na kurkusa, inda zuwan shi ke da wuya suka shawarce shi akan mika shi asibiti domin kulawa da lafiyar sa kafin a cigaba da binciken lamarin sakamakon girman raunin da ya samu.

Shi kuwa alkalin kotu Siyanbola, ya zartar da hukuncin dauri na shekara biyar kan Olaniyan sakamakon girman laifin da ya aikata.

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng