An tsinto gawar 'yan Matan Najeriya 26 a tekun Kasar Italiya

An tsinto gawar 'yan Matan Najeriya 26 a tekun Kasar Italiya

Hukumar jami'an tsaro ta kasar Italiya ta na binciken yadda aka tsinto gawarwakin matan Najeriya 26 a wani tekun Kasar wanda mafi yawancin su budurwai ne.

Hukumar ta na zargin wannan mata da aka tsinto gawarwakin su cewa an keta musu haddi da kuma kisan gilla da aka yi musu a yayin da suke yunkurin ketare tekun bahar maliya.

Legit.ng ta ruwaito da sanadin jaridar The Nation cewa, an tambayoyi masu yin kaura biyar a tashar jiragen ruwa ta Salerno dake kudancin kasar Italiya inda suka bayyana cewa, wani jirgin ceto na kasar Andalus mai sunan Cantabria ne ya dauko wannan gawarwaki tare da masu yin kaura 375 da aka ceto.

'Yan jaridu na kasar italiya sun wallafo cewa, an killace wannan gawarwakin ne a wani sashe mai na'urarar sanyayay daki dake cikin jirgin , wanda mafi yawancin matan basu wuci shekaru 14 zuwa 18 ba.

Rahotanni daga jaridar La repubblica ta ruwaito cewa, mafi yawancin mutane 375 wadanda aka ceto 'yan nahiyar Afirka ne da suka hadar da kasashen Najeriya, Senegal, Ghana, Gambia da kuma Sudan.

An tsinto gawar 'yan Matan Najeriya 26 a tekun Kasar Italiya
An tsinto gawar 'yan Matan Najeriya 26 a tekun Kasar Italiya

Jaridar ta ci gaba da cewa, cikin wannan mutane akwai mata 90 wanda 8 daga cikin su suna dauke da juna biyune da kuma kananan yara 52.

Sai kuma anan gida Najeriya inda hadima ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkokin kasashen ketare Misis Abike Dabire ta bayyana cewa, wannan abu ne mai karya zuciya tare da yin kaico da Allah wadai.

KARANTA KUMA: Hanyoyin inganta Lafiya 7 da Namijin Goro ke yi a Jikin dan Adam

Ta ke cewa, "kasar Najeriya tana bukatar a fara wayar da kan al'ummomin ta akan ire-iren hadurran dake tattare da wannan salo na yin kaura zuwa wasu kasashen".

"Gwamnatin Shugaba Buhari ta cigaba da fadi tashi tare da hadin gwiwar hukumar yin kaura ta duniya wajen maido da 'yan kasar Najeriya gida da suka bukaci dawowa, wanda a yanzu adadin wadanda suka dawo kimanin 5000 cikin watannin shidda da suka gabata, inda suka yi da na sanin yin kaura tun a farko sakamakonirin wahalhalun rayuwa da suka tsinci kawunan su".

A karshe hadimar take cewa, "tana mika sakon gaisuwar da kuma bayar da hakuri ga 'yan uwan wadanda suka yi wannan rashi, tare da gargadin al'ummar najeriya wajen gujewa fadawa ire-iren wannan hadurra."

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Goron gayyata: Labari da duminta: Jaridar Legit.ng Hausa ta kawo maku hanya mafi sauki da zaku iya karanta labaranta

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng