YANZU-YANZU: Jami’ar Kashere ta rufe makarantar saboda jinkirin biya albashi
- Jami’ar Kashere ta tarayya ta fara yajin aika na wucen gadi a yau Litinin
- Kwamitin JAC ta ce yajin aikin nada nasaba da jinkirta biya albashin ma’aikata
- JAC ta bayyana cewa wannan gargadi na makonnin 3 ne kawai
Kwamitin hadin gwiwar aikace-aikace (JAC) na jami'ar Kashere ta tarayya wanda ke jihar Gombe ta fara yajin aiki na makonnin uku don nuna rashin amincewarsu da jinkirin biya albashin watan Oktoba na wanan shekara.
Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, kwamitin ta yanke wannan shawarar fara yajin aiki na wucen gadi a yau ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba a lokacin wani taron da aka gudanar.
Idan dai baku manta ba a ranar 17 ga Satumba ne kungiyar malaman jami'o'i a Najeriya, ASUU ta sanar da dakatar da yajin aiki na makonni biyar.
KU KARANTA: Lokacin jin dadi da warwasawa na daf zuwa - Inji gwamnatin tarayya
Amma ƙungiyar ta bayyana cewa dakatarwa yana da lokaci don gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma.
Ku saurari cikakken bayani nan gaba ....
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng