Adama Indimi ta sha Maltina cikin jirgin sama

Adama Indimi ta sha Maltina cikin jirgin sama

A kullun tsadadden rayuwar masu kudi kan ba yan Najeriya masu rufin asiri shaáwa saboda wasu dalilai masu birgewa. Kowa na iya burin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa a kasar waje kamar ahlin Indimi da suka yi bikin zagayowar ranar haihuwar mahaifinsu karo na 70 a kasar Spain da Paris inda suka shafe makonni.

Abun kan zamo kamar tatsuniya idan akace masu kudin kan je duk inda zasu cikin jirgin sama. Amma baa bun mamaki bane idan akayi la’akari da yawan dukiyar mahaifin su.

A wani sabon hoto, an gano sarauniyar mai tashen kyau zaune cikin jirgin saman su, tana shan lemun Maltina. Batayi la’akari da tsadadden kayan da ta sa hade da jakar ratayawa tsadadde, kyakywar ta sha lemun maltina wanda kowa ya san mai arha ne cikin farin ciki.

Adama Indimi ta sha Maltina cikin jirgin sama
Adama Indimi ta sha Maltina cikin jirgin sama

An yada hoton ne a shafinta na zumuntaa, inda ta nuna cewa tayi alfahari da farin ciki da wannan lemu da aka shayar da ita.

KU KARANTA KUMA: Buratai ya rubuta wasika na musamman don ba da tabbaci ga sojoji

Hakan ya nuna cewa lemun maltina ya dinke Baraka tsakanin masu kudi da talakawa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng