Wata 'yar jami'a ta haifi 'yan 3 a garin Kalaba
Wata daliba a jami'ar dake kwalejin koyon karatun aikin lafiya ta jihar Abia, garin Aba dake a kudu maso gabashin kasar nan mai suna Felicia Ifeanyi ta samu haihuwar 'ya'ya uku ringis a asibitin koyarwa ta jami'ar Kalaba, jihar Kuros Ribas.
Ita dai mai jegon, Felicia, tana zaune ne a karamar hukumar Akamkpa a garin Uhet na jihar ta Kuros Ribas sannan kuma ta bayyana matukar mamakin ta yayin da aka ce 'yan uku ne za ta haifa inda ta bayyana hakan a matsayin baiwa daga Allah.
KU KARANTA: Yau ake sa ran za'a karbi tubar Rahma Sadau
Legit.ng ma ta samu a nashi bangaren, mijin na mai jegon, Okechuku shima ya bayyana matukar jin dadin sa tare da nuna godiyar sa ga Allah da ya bashi kyautar 'ya'yan.
To amma sai dai ma'auratan sun bukaci da jama'a su taimaka masu wajen hidimar 'yayan don kuwa mijin yace bashi da abun yi don haka ya cikin matukar bukata.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng