Mutane 9 sun tsallake rijiya da baya a wani hatsarin Babbar mota da tayi matashi da kananun motoci 2 a jihar Legas
A ranar Jumma'ar da ta gabata akalla mutane 9 sun tsallake rijiya da baya a wani hatsari da ya afku, yayin da wata babbar mota ta danne kananin motoci biyu a wata babbar hanyar jihar Legas.
Rahotanni da sanadin wadanda abin ya faru a gaban su sun bayyana manema labarai cewa, hatsarin ya faru ne a babbar hanyar Ikorodu ta jihar, inda motoci biyu suka hadu kuma kowace tayi kundunbala sa'annan ta dawo kasa.
KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya 500 su na garkame a gidajen kaso na kasar Sin
Wani wanda abin ya faru a gaban shi da ya bayar da sunan shi na Charles ya bayyana cewa, wata babbar mota da abin bai shafa ta zo daga baya ta yi matashi da wannan motocin biyu da suka gamu tun a fari.
Ya kara da cewa, an kaiwa mutane tara dauki na gaggawa dake cikin motocin kuma kowanen su na cikin koshin lafiya a yanzu.
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng