Dandalin Kannywood: Jaruma Ai'sha Tsamiya ta sharara karya a bainar jama'a

Dandalin Kannywood: Jaruma Ai'sha Tsamiya ta sharara karya a bainar jama'a

A cikin wani lamari mai matukar kunya da dariya, an bankado jirgin fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood mai suna Ai'sha Aliyu da aka fi sani da Tsamiya inda aka gano cewar jarumar ta sharara karya ne kawai a bainar jama'a a cikin wani shiri na gidan Talabijin na Arewa24.

Mun samu dai cewa a kwanan baya ne jarumar ta sanar da samun gurbin karatun ta a budaddiyar jami'ar nan ta gwamnatin tarayya da ake yiwa lakabi da National Open University (NOUN) a turance domin ta yi karatun kimiyyar lafiya watau Health Technology.

Dandalin Kannywood: Jaruma Ai'sha Tsamiya ta sharara karya a bainar jama'a
Dandalin Kannywood: Jaruma Ai'sha Tsamiya ta sharara karya a bainar jama'a

KU KARANTA: Yadda kauna ta sa ba baro iyaye na don in sadu da Adam A. Zango

Legit.ng amma ta samu daga majiyar mu cewa ba a yin wannan kwas din a jami'ar kamar dai yadda Daraktan Watsa Labarai na jami'ar, Malam Ibrahim Sheme, ya fada wa majiyar ta mu.

Da yake karin haske, jami'in yada labarai na jami'ar ya kuma bayyana cewa watakila dai jarumar na so ne ta cewa Public Health don kuwa shine kadai kwas din da jami'ar ke koyarwa da ya danganci lafiya.

Daga nan ne kuma sai ya jinjinawa jarumar game da yadda take da zummar yin karatu ba kamar sauran wasu matan ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng