Yadda maigadi da wasu malamai ke lalata tarbiyar Dalibai a wata sakandiren tarayya ta Mata zalla

Yadda maigadi da wasu malamai ke lalata tarbiyar Dalibai a wata sakandiren tarayya ta Mata zalla

Bincike ya tona asirin yadda Dalibai mata a sakandiren gwamnatin tarayya dake Langtang a Jihar Filato ke fita daga makaranta domin haduwa da duk wani namiji mai bukatar su.

Wani abun haushi a wannan dake faruwa a wannan makaranta shi ne, bayan hada baki da akeyi da maigadi wajen shige da ficen daliban, wasu daga cikin malamai ma na kiran daliban zuwa ofishinsu yayin karatun dare ko kuma gayyatar daliban zuwa gidajensu domin yin hutun karshen sati tare da su.

Yadda maigadi da wasu malamai ke lalata tarbiyar Dalibai a wata sakandiren tarayya ta Mata zalla
Yadda maigadi da wasu malamai ke lalata tarbiyar Dalibai a wata sakandiren tarayya ta Mata zalla

Binciken jaridar TheCable da shafin jaridar drumbeatnews.co.uk ya kwarmata ya bayyana cewar wani hatsabibin maigadi ne a makarantar ke kawalcin daliban ga duk mai bukata, matukar dai za a ba shi naira dubu biyar.

DUBA WANNAN: Hotunan gwamna Ganduje cikin gamagarin jama'a a jirgin sama na haya

Binciken ya nuna yadda hukumar makarantar taki amincewa da faruwar wanna lamari duk kuwa da shaidun da yan jaridar suka gabar ma ta. Saidai wata daga cikin shugabannin kungiyar tsofin dalibai ta bayyana cewar sun taba samun rahoto makamancin wannan amma su ma koda suka tunkari hukumar makarantar sai tayi watsi da zargin ba tare da gudanar da wani bincike ba.

Kamfanin jaridar ta TheCable ya ce ya tuntubi ma'aikatar ilimi ta kasa a kan wannan badakala dake faruwa a wannan makaranta, saidai hukumar ta nemi su aiko mata rahoton binciken a rubuce tare da duk hujjojin da suke da su. Kamfanin jaridar yaci alwashin tona asirin duk masu hannu cikin wannan cin amanar iyayen yara.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng