Najeriya da Rasha sun saka hannu kan yarjejeniyar samar da makamashin Nukiliya
Kasar Rasha ta cimma wata yarjejeniya da Najeriya domin ginaw tare da sarrafawa Najeriya makamin Nukiliya domin samar da wadatacciyar wutar lantarki.
Wani kamfanin sarrafa makamashin Nukiliya dake Rasha, Rosatom, ya tabbatar da hakan tare da sanar da cewar a yanzu haka suna gudanar da bincike domin samun inda ya dace a kafa makamashin na Nukiliya tare da kiyasin kudin da aiki zai lashe.
Tun a shekarar 2015 Najeriya ta fara tattaunawa da kamfanin na Rosatom domin samar da sansanin makamashin Nukiliya ga Najeriya guda hudu a kan kudi Dala biliyan 20, kamar yadda hukumar sarrafa makamashi ta kasa ta bayyana.
DUBA WANNAN: Cikin Hotuna: Hukumar NNPC da hadin gwuiwar kamfanin E&P sun kaddamar da shirin bunkasa tattalin arzikin Najeriya
Najeriya, kasar data fi duk ragowar kasashen Afrika yawan jama'a, na samar da adadin megawat 4,500 ne kacal na lantarki.
Kamfanin Rosatom zai gina sansanin makamashin Nukiliya a kasashen Afrika da dama da ya hada da kasar Afrika ta Kudu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng