Dandalin Kannywood: Yadda kauna ta sa na baro iyaye na na taho ganin Adam A. Zango - Amina Amal
A cikin wata fira da jarumar nan ta wasan fim din Hausa mai suna Amina Muhammad da ake yi wa lakani da Amal ta yi da 'yan jarida, ta zayyana tiryan-tiryan yadda matukar kauna ta sa ta baro iyayen ta a kasar Kamaru ta taho Kaduna ganin Adam A. Zango.
Jarumar da ta bayyana cewa an haife ta ta kuma yi dukkan rayuwar ta har girmanta a kasar Kamaru, ta bayyana cewa jarumin da take matukar kauna duk a cikin 'yan fim shine Adam A. Zangon da ta ce shine ma musabbabin baro iyayen nata don dai kawai ta yi ido biyu da shi.
KU KARANTA: Allah yayi wa matar Sanata Goje rasuwa
Legit.ng dai ta samu cewa a cikin firar, Amal ta bayyana yadda tayi ta dauki ba dadi da iyayenta kafin su amince su barta ta taho wurin jarumin inda ta ce daga baya dai dole suka kyale ta saboda sun ga shine babban burin ta a rayuwa.
Haka ma dai jarumar ta bayyana cewa babban dalilin da yasa ta fara fim kuwa shine saboda ta tabbatarwa da kawayen ta da ma dukkan wanda ya santa cewar tabbas ta hadu da jarumin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng