Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Boss Mustapha, sabon Sakataren gwamnatin Buhari

Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Boss Mustapha, sabon Sakataren gwamnatin Buhari

A yau ne dai al'ummar Najeriya suka tashi da jin wani labari mai ban sha'awa yayin da suka samu cewa shugaba Muhammadu Buhari ya amince da korar Sakataren gwamnatin sa Mista Babachir Lawal tare da shugaban hukumar leken asirin tarayyar Mista Ayo Oke gaba daya.

Haka ma dai sanarwar korar ta jami'an da ta fito daga bakin mai magana da yawun shugaba Buhari din Femi Adesina ta kuma sanar da cewa tuna har shugaban ya nada sabon Sakatare mai suna Boss Mustapha.

Legit.ng ta lalubo maku wasu muhimman al'amurra da ya kamata ku sani game da sabon Sakataren:

Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Boss Mustapha, sabon Sakataren gwamnatin Buhari
Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Boss Mustapha, sabon Sakataren gwamnatin Buhari

KU KARANTA: Real Madrid sun kunyata a hannun 'yan jagaliya

1. Da farko dai cikakken sunan sa shine Boss Gida Mustapha kuma ya fito ne daga jihar Adamawa dake a Arewa maso gabashin kasar nan.

2. Mun samu haka zalika kuma cewa Boss Mustapha kwararren lauya ne dake da sanin makamar aiki sosai da kuma yayi aiki a gwamnatance da kuma matsayi na mai zaman kansa.

3. Kafin wannan sabon mukamin nasa dai, Boss Mustapha shine shugaban hukumar nan dake kula da hanyoyin jiragen ruwa na cikin kasa watau National Inland Waterways Authority (NIWA).

4. Boss Mustapha babban dan siyasa ne da ya taba rike matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar CAN ta kasa baki daya a shekarun baya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng