Yan mata 2 sun tada bama-bamai a garin Madagali, jihar Adamawa
Labarin da muke samu daga majiyar mu na nuni da cewa wasu yan mata dake kyautata zaton 'yan kunar bakin wake ne sun tarwatsa kansu da kansu a yayin wani harin kunar bakin waken da suka so sukai amma basuyi nasara ba a kauyen Magar dake karamar hukumar Madagali, jihar Adamawa.
Kamar dai yadda wasu shaidun gani da ido suka shaidawa majiyar tamu, yan matan sun tarwatse ne bayan da jigidar bama-baman su ta tashi a safiyar ranar Asabar kafin su ida isa inda suka so su kai harin.
KU KARANTA: Najeriya na fuskantar matsancin rabuwar kai - Atiku
Legit.ng dai ta samu cewa shugaban karamar hukumar ta Madagali Muhammad Yusuf ya tabbatar da faruwar lamarin a wata fira da yayi da 'yan jarida.
Karamar hukumar ta Madagali dai na daya daga cikin kananan hukumomin da 'yan ta'addan Boko Haram suka taba kwacewa a shekarun baya da kuma sojojin Najeriya suka kwato ta bayan hawan mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng