Yanzu-yanzu : Hafson rudunar sojin kasa ya halarci taron bikin rufe attisayen murmushin kada
- Buratai ya halarci bikin rufe attisayen murmushin kada karo na 2
- A kaddamar da attisayen ne dan kawo karshen tsagerun Neja Delta dake fasa bututun mai a yankin kudu maso kudu da kudu maso gabas
A yau litinin 30 ga watan Okotoba attisayen murmushin kada karo na 2 ya zo karshe.
Rundunar sojin Najeriya ta fara atisayen murmushin kada karo na biyu tun a watan Mayu na shekara 2016 dan kawo karshen matsalar tsagerun Neja Delta da ke fasa bututun mai, da sauran na’o’in ta’adancin da ya addabin yankin kudu maso kudu da kudu maso gabas.
An gudanar da bikin ne a shelkwatar rudunar soji na Division 6 dake Igwurruta, birnin Fatakol a jihar Rivas.
KU KARANTA : Osinbajo ya ci amanar Coci da Kristoci saboda ya hada kai da Buhari - Fani-Kayode
Hafson rundunar sojin Najeriya Lt Janar TY Buratai wanda ya halarci taron bikin rufe attisayen, ya ce rundunar sojin Najeriya na yan Najeriya ne, wanda burinta shine kare hakki da mutuncin yan Najeriya kuma ba za ta taba cin mutuncin su ba.
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng