Lafiya uwar jiki: Anfanin kokumba 4 wajen gyaran fatar dan adam
Gurji ko kuma kokumba na dauke da sinadaren magance gautsin fata sannan yana taimakawa wajen sanyafa fata sheki da laushi.
Kamar dai yadda muka saba, Legit.ng ta tattaro maku wasu tarin anfanin na kokumba har guda shida wajen gyaran fata musamman ma ga mata 'yan kwalisa:
1. Domin rage kiba ko tumbi: Bincike ya nuna cewa idan har aka markada bawon kokumba aka markada aka hada da lemun tsami da citta to tabbas za'a rage kiba.
2. Maganin kurajen fuska: Haka ma dai idan aka markada ta aka rika shafawa a fuska, to tana maganin kurajen fuska.
KU KARANTA: Yadda akw miyar kwakwa
3. Hasken fata: Ina masu son su kara hasken fata? Idan aka rika shafa ruwan kokumba a fuska da wuya a barshi yayi akalla mintuna 10 to tabbas za'a kara haske.
4. Maganin kodewar fata: Idana aka markada kokumba aka kuma hada ta da kindirmon nono da garin alkama aka rika shafawa za'a ga ikon Allah.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng