Yadda ake Miyar Kwakwa
Ana iya cin Miyar da kowanne nau'i na abinci.
Abubuwan da ake bukata
1. Kwakwa daidai da bukatar ku
2. Markadadden kayan Miya
3. Nama ko Kifi
4. Garin Kori
5. Mai
6. Tafarnuwa
7. Tayim( Thyme)
8. Sinadaran dandano
DUBA WANNAN: Hotunan gwamnan Ganduje cikin gamarin jama'a a jirgin sama na haya
Yadda ake yin Miyar
A kankare Kwakwa sannan a wanke ta fes sai a markadeta a ajiye gefe guda.
A dora Mai a kan wuta a soya shi da tafarnuwa, amma ba tare da barin tafarnuwar ta kone ba. Yana da kyau a rage wuta yayin suyar man da tafarnuwa.
A zuba markadadden kayan Miya cikin soyayyen man. A kara soyayyen ko dafaffen Nama ko Kifi bayan kayan Miyar ya soyu. A kara kayan dandano dana kamshi a barsu su turara. Sai a kawo ruwan Kwakwa da aka tace a zuba, sai a rufe a barshi ya dan dahu domin miyar tayi kauri. Sai a sauke bayan tayi kauri yadda ake bukata.
A ci dadi lafiya.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng