Dandalin Kannywood: Jaruma Halima Atete ta gamu da masoyin ta Sanata Kwankwaso a Dubai

Dandalin Kannywood: Jaruma Halima Atete ta gamu da masoyin ta Sanata Kwankwaso a Dubai

Wani hoton da ya bulla a dandalin zumunta a satin da ya gabata na ci gaba da daukar hankulan jama'a da dama na Jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa Halima Atete da kuma tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a filin jirgi.

Hoton dai na kunshe ne da jarumar zaune a kusa da shahararren dan siyasar inda ta dora wata jar hula da ke nuna alamun mubayi'a ga bin tafarkin Kwankwasiyya karkashin jagorancin tsohon Gwamnan.

Dandalin Kannywood: Jaruma Halima Atete ta gamu da masoyin ta Sanata Kwankwaso a Dubai
Dandalin Kannywood: Jaruma Halima Atete ta gamu da masoyin ta Sanata Kwankwaso a Dubai

KU KARANTA: Gwamnan Kogi ya haramta kungiyoyin fafutuka a jihar sa

Legit.ng dai ta samu daga majiyoyi da dama cewa an dauki hoton ne a filin sauka da tashin jirage na kasa-da-kasa dake a garin Dubai a dunkulalliyar Daular Larabawa.

Da ma dai ba tun yauba jaruman dake shirya fina-finai a jihar ta Kano din suna nuna matukar kaunar su ga tsohon Gwamnan da suke kallon yana maraba da sana'ar ta su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng