Daga baya kenan: Rahama Sadau ta nemi afuwan ƙungiyar yan Fim ta ƙasa

Daga baya kenan: Rahama Sadau ta nemi afuwan ƙungiyar yan Fim ta ƙasa

Fitacciyar jarumar fina finan Kannywood din nan data shahara wajen iya tikan rawa kamar mazari, Rahama Sadau ta nemi afuwar kungiyar kula yan Fim ta kasa, MOPPAN dangane da dakatar da ita da suka yi.

Premium Times ta ruwaito tun a shekarar data gabata ne MOPPAN ta sallami Rahama Sadau daga harkar Fim sakamakon wani bidiyon waka data fito a ciki, wanda aka hangeta tana rungumar wani mawaki mai suna ClassiQ.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta musanta batun wata alaƙa tsakanin Buhari da Maina

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasikar da Rahama Sadau ta aike ma MOPPAN na neman afuwa na kunshe da magiya tare da nuna nadamar abubuwan da suka faru a baya, inda ta roki a mayar da ita harkar Fim.

Daga baya kenan: Rahama Sadau ta nemi afuwan ƙungiyar yan Fim ta ƙasa
Rahama Sadau

Sai dai sallamar da aka yi ma Rahama Sadau ya kara haskaka tauraron ta, inda shahararren mawakin kasar Amurka, Akon ya gayyace ta zuwa Amurka don samun gurbi cikin wani Fim dinsa.

“Dan Adam ajizi ne, don haka zan iya yin kuskure, don haka a matsayita na yarinya, ina rokon kafatanin yan Fim, shuwagabannin kungiyoyin Fim, al’ummar Arewa da kuma yan kallo daku yafe min,” Inji Rahama.

Sakataren MOPPAN, Salisu Mohammed ya bayyana ma majiyar mu cewa “Zamu yi zaman tattauna wasikar tat a, don daukan matsaya guda akan batun. Amma fa tayi maganganu marasa dadi a baya, wanda basu dace ba.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng