Wasu matasa da suka lakaɗa ma ‘Ɗan shafi mulera’ duka sun gamu da fushin Kotu

Wasu matasa da suka lakaɗa ma ‘Ɗan shafi mulera’ duka sun gamu da fushin Kotu

Wasu Matasa da suka casa wani mutumi kan zarginsa akan aikata ma wani mutumi shafi mulera sun shiga hannu hukuma, inda aka gurfanar dasu gaban Kotun majistri dake Ikeja, jihar Legas.

Rundunar Yansanda ta gurfanar da Salihu Bala, Alhassan Mohammed tare da Masa’udu Abubakar dukkaninsu yan shekaru 20, kamar yadda kamfanin dillancin labaru ta ruwaito.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta musanta batun wata alaƙa tsakanin Buhari da Maina

Ana zargin matasan ne da tikan wani mutumi mai suna Gbenga Afuye a tashar motar Ogba dake jihar Legas a ranar 25 ga watan Satumba, kamar yadda dansanda mai kara, Victor Eruada ya shaida ma Kotu.

Wasu matasa da suka lakaɗa ma ‘Ɗan shafi mulera’ duka sun gamu da fushin Kotu
Wasu matasa

“Taron dangi suka yi ma Gbenga, inda suka ji mai ciwo a baki, daga bisani jama’a suka kai kararsu zuwa ga Yansanda, sa’annan jami’an Yansanda suka cafke su.” Inji Dansandan.

Sai dai matasan sun musanta wannan tuhuma da aka yi musu, hakan ta sanya ALkalin Kotu ya bada belinsu akan kudi Nairi 50,000 kowanne, tare da wadanda zasu tsaya musu mutum daya akan kowanne.

Daga nan sai alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba don cigaba da sauraron karar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng