Labari cikin Hotuna: Yadda taron shugaba Buhari a birnin Niamey ya kasance
Kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ruwaito a shafin sa na dandalin sada zumunta na facebook cewa, ya halarci taro na 4 na shugabannin kasashen nahiyyar Afirka ta Yamma (ECOWAS) akan daidaita kudin kasashen ya zamto guda.
Shugaba Buhari ya yi kira ga kasashen na ECOWAS akan su yi taka-tsan-tsan wajen ci gaba da yunkurin daidaita kudaden kasashen ya zamto guda zuwa shekarar 2020.
Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya yi gargadi a taron akan a yi la'akari da yanayin tattalin arzikin kasashen tare da daukar izina akan ire-iren abubuwan dake faruwa a kungiyar kasashen turai (European Union).
Ya ke cewa, Najeriya za ta yi taka-tsan-tsan wajen ci gaba da yunkuri domin daidaita kudin a maimakon ta yi watsi da ababe masu muhimmanci.
Buhari ya ce, "Mu a tamu mahangar, kasashen ECOWAS ba su kai matakin shiryawa daidaiton kudi ba, kuma wannan tana daya daga cikin abun damuwa ga Najeriya.
Ba za mu gaggawa ba don kawai muna son a samu daidaiton kudi, domin kuwa akwai aiki babba da yake gaban mu kuma yake bukatar aiwatarwa."
KARANTA KUMA: Akwai yara miliyan 264 da ba su zuwa makaranta - UNESCO
"Hangen nesan Najeriya a yanzu shine, kafa kwamitin kwararru da su leka kuma su hango cikin wannan lamari, domin kuwa ba abu ne karami ba."
Shugaba Buhari ya kara da cewa, wannan manufa ce mai bankaye wanda Najeriya za ta shige gaba wajen wanzuwar wannan lamari, sai dai hanzari ba gudu ba shine a yi duba zuwa ga kalubale da kowace kasa take fuskanta kuma a kawo hanyoyin warware su.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng