Harkallar maido Maina aiki: Takashin Malami da Dambazau ta duri ruwa
Rahotannin sirri da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni da cewa ya zuwa yanzu kam hankulan Ministocin shugaba Muhammadu Buhari da suka hada da Abubakar Malami da Abdurrahman Dambazau sun riga sun gama tashi don kuwa akwai yi wuwar shugaban ya ladabtar da su.
Su dai wadannan ministocin na Buhari ana zargin cewa sune suka taka muhimmiyar rawa suka kuma yi ruwa da tsaki wajen tabbatar da maido da korarre kuma mai babban laifin nan da hukumar EFCC ta dade tana nema Abdurrasheed Maina aiki har suka ma bashi mukamin Darakta.
KU KARANTA: Da gwamnatin Buhari da ta Jonathan duk abu guda ne
Legit.ng dai ta samu cewa tun jiya ne dai shugabar ma'aitan gwamnatin tarayyar ta gabatar da bayanan yadda akayi aka maida Abdurrasheed Maina aiki bayan ta kore shi kamar dai yadda shugaban kasar ya nema.
To ana dai zaton cewa a kowane lokaci daga yanzu shugaba Buhari din zai kira ministocin biyu domin yaji daga bakin su su kuma game da harkallar kafin daga bisani ya yanke hukuncin da yaga ya fi dacewa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng