“Allah ya kiyaye, ba zamu taba yarda da wannan lalacin ba”
- Zazzafar cecekuce ta barke a masarautar Saudiyya
- Hakan ya biyo bayan kudirin kasar na bude gidajen sinima
- Wani Shehin malami yace bazasu amince da hakan ba
- A cewar sa hakan ba komai bane face lalaci da kuma yada sabo a doron duniya
Rahotanni sun kawo cewa wani zazzafar sabani ya barke a kasar Saudiyya, saboda dokin naki da babban shehin malami wato Mufti Sheikh Abdul-Aziz Ibn Al sheikh ya hau, domin kulabalantar kudirin masarautar kasar dauka na bude gidajen sinima.
Da yake jawabi a gidan talabijin Al Majid, shehin malamin ya ce : “Allah ya kiyaye, ba zamu taba da yarda da wannan lalacin ba. Bukukuwan wake-wake da kuma nuna fina-finai ba komai ba ne, face lalaci da kuma yada sabo a doron duniya”
Kalubalantar lamarin da shehin malamin ya yi ya haifar da zazzafan cece-kuce tsakanin ‘yan kasar Saudiyya, inda tuni wasu suka yi wa babban malamin kudin goro da kuma tuhumar sa da zama dan tsatstsaucin ra’ayi.
KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya na Allah-Allah PDP ta dawo mulki – Tsohon mataimakin Obasanjo
Masarautar Saudiyya dai ta yi kunnen uwar shegu game da hannunka mai sanda da malamin ya yi, inda tuni ta bai wa al’umarta izinin zuwa gidajen kallo.
Sheik Abdul-Aziz wanda ke ci gaba da yin ruwa da tsaki a wajen kare martabar Musulunci a duniya, ya koka sosai da wannan sabuwar turbar da Saudiyya ta hau.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng