Cikar Kwankwaso shekaru 61: Ina taya ka murna, Allah ya ƙara basira – Inji Ganduje

Cikar Kwankwaso shekaru 61: Ina taya ka murna, Allah ya ƙara basira – Inji Ganduje

- Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yaba ma Kwankwaso

- Masana siyasa sun ce 'ta ciki, na ciki'

Duk da irin tsatstsamar alakar siyasa dake tsakanin Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, an jiyo gwamnan yana yaba ma Kwankwaso.

Ganduje ya yaba ma Kwankwaso ne yayin da tsohon Maigidan nasa ke bikin cika shekaru 61 a rayuwa, inda aka haife shi a ranar 22 ga watan Oktoban 1956, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Yan ƙunar baƙin wake sun kai hari garejin mota a Maiduguri, mutane da dama sun mutu

A yayin bikin ne gwamnan jihar Kano ya aika da sakon taya murna ga Kwankwaso, a wata jarida, inda yake yaba masa, tare da yi masa addu’ar samun tsawon rai da shekaru masu albarka.

Cikar Kwankwaso shekaru 61: Ina taya ka murna, Allah ya ƙara basira – Inji Ganduje
Sakon taya murna

“A madadi na, iyalai na da kuma al’ummar jihar Kanom muna taya mai girma tsohon gwamna Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 61.

“Ina yi maka fatan karin lafiya da tsawon kwana, tare da fatan Allah ya kara maka basira da kishin kasa, ta yadda jihar Kano da Najeriya zata ci amfaninka.” Inji Gwamna Ganduje.

Masu bibiyan al’amaurar siyasar jihar Kano sun yi mamakin wannan sakon taya Kwankwaso murna daya fito daga bakin gwamna Ganduje, inda suke ganin anya kuwa, ba ta ciki na ciki ba kuwa?

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Kalli aikace aikacen gwamna Ganduje a Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng