Wani mutum ya tsunduma a cikin tekun jihar Legas
Akwai wani dan karamin tashin hankali a gadar dake babbar hanyar Lekki zuwa Ikoyi yayin da wani mutum wanda har yanzu ba fayyace ko waye ba ya tsunduma cikin tafkin jihar ta Legas daga saman gadar.

Legit.ng ta ruwaito daga jaridar The Nation cewa, wannan abu ya faru ne a ranar Jumma'a 20 a watan Oktoba, ya yin da ma'aikata na cibiyar kawo agaji na gaggawa da masu ruwa da tsaki dake wajen yayin da abin ya faru su ka dugunzuma domin ceto wannan mutum.
KARANTA KUMA: Kiris ya ragewa Najeriya ta yi rugu-rugu - 'Yan Majalisa
Cibiyar kawo agajin gaggawa ta Lagos State Emergency Management Agency, LASEMA, da jami'an 'yan sanda na ruwa sun tabbatar da faruwar wannan tabokara da wannan mutumi ya yi.

Sai dai an yi rashin sa'ar gano ainihin sunan wannan mutum, domin a lokacin hada labarai ana ta kokarin yadda za'a lalubo shi cikin tekun.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng