Dandalin Kannywood: Takaitaccen tarihin mahaifiyar Ali Nuhu

Dandalin Kannywood: Takaitaccen tarihin mahaifiyar Ali Nuhu

A yau Legit.ng ta kawo muku dan takaitaccen tarihin mahaifiyar jarumi Ali Nuhu tare da wata 'yar gajeruwar hikaya da dan na ta a lokacin rayuwar ta.

Sunan mahaifiyar jarumi Ali dai Hajiya Fatima Karderam Digema, wadda 'yar asalin garin Bama ce dake jihar Borno.

Sakamakon haka ne jarumin ya yi amfani da sunan mahaifiyar ta sa wajen sanyawa kamfanin sa na shirya fina-finai sunan FKD wato dai ma'anar sunan mahaifiyar domin tunawa da ita. Jarumin ya kuma sanyawa 'yar sa ta farko sunan Fatima duka don ya samu damar tunawa da wadda ta yi sanadin zuwan sa duniya.

Dandalin Kannywood: Takaitaccen tarihin mahaifiyar Ali Nuhu
Dandalin Kannywood: Takaitaccen tarihin mahaifiyar Ali Nuhu

A takaice yanzu shekara 18 kenan da rasuwar mahaifiyar ta sa, wanda shine adadin shekarun da jarumi Ali Nuhu ya yi yana sana'ar fim, wanda kafin rasuwar ta sai da ta baiwa dan na ta damar shiga wannan harka tare da neman ma sa tabarraki daga wurin Mahalicci.

KARANTA KUMA: Yadda jihohi 36 na Najeriya su ka batar da Naira Biliyan 2.67 domin rage bashin dake kan kasar

A yayin ganawa da marubuta mujallai jarumi Ali Nuhu ya bayyana cikin barkwanci cewa, mahaifiyar ta sa ta na kiran shi da sunan Ali sarkin Matsala wanda sanadiyar hakan ne bayan ta siyo mi shi tsarabar riga a wata tafiya kasar Amurka da ta yi, aka sanya ma sa sunan Ali Official Trouble Maker a bayan taguwar.

Daga karshe an yiwa mahaifiyar addu'a da cewar Allah ya kara haske a kabarin ta da kuma jin kan ta.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng