Sojojin Najeriya sun yi artabu da tsagerun Neja Delta, sun ƙwata Makamai (Hotuna)
Sojojin Najeriya dake gudanar da aiki na musamman a yankin kudu maso kudancin kasar nan, ‘Murmushin Kada II’ sun kai samame wani sansanin tsagerun Neja Delta a ranar Talata 17 ga watan Oktoba.
Jaridar Sahara Reporters tace Sojojin na gudanar da aikin su ne a tsakanin garuruwan Ajakurama, Gelegele da Egbema a karamar hukumar Warri ta Arewa a lokacin da suka ci karo da wannan sansani.
KU KARANTA: Kica-kican ma’aurata: Kotu ta sako yaron Atiku Abubakar, ta ƙwace Ýaýansa
Sai dai majiyar Legit.ng ta shaida cewa da hangen Sojojin, sai tsagerun suka ranta ana kare, daga nan ne sai Sojojin suka caje sansanin inda suka binciko makamai, sa’annan suka kona sansanin duka.
Wani mazaunin garin ya bayyana ma majiyar mu cewa sun ji dadi da zuwan Sojojin garin, da har kuma suka samu nasarar fatattakar tsagerun dake yankin, inda yace:
“Garin Ajaruma na fama da ayyukan yan ta’adda, shi yasa Sojoji suka fatattake su, a yanzu haka shuwagabanninsu kamar Blessing Magic, Godwin Namu, Felix Odowu, Osuwo Osiya da kuma Double Prince sun gudu daga garin.”
Shima Sarkin Egbema, G.E.O Tiemo ya tabbatar da samamen, inda yace “Duk da cewa Tsagerun sun sha alwashin dawowa, ya zama dole in jin jina ma shugaban su, Koko, saboda namijin kokarin da suka yi.”
Daga cikin abubuwan da gano a sansanin akwai alburusai, bindigar AK-47 guda 3, wayar hannu, Radio, na’urar Go Tv, DVD, kayan Sojoji da kuma rigar shiga ruwa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng