Allah da girma yake: Wasu mata 3 sun karbi addinin musulunci a jihar Bauchi
Legit.ng ta kawo muku rahoton wasu mata uku da suka karbi kalmar shahada a kauyen Tilden Fulani dake karamar hukumar Torro ta jihar Bauchi.
A yau Laraba 18 ga watan Oktoba na shekarar 2017, wanda hausawa kan ce Tabawa ranar samu domin kuwa musulmai sun samu karuwa, inda wannan mata suka kabi addinin musulunci hannu biyu-biyu tare da sauya musu suna zuwa irin na salihan bayi.
KARANTA KUMA: Kasancewar shugaba Buhari Ministan man fetur ba matsala ba ce - Wani Dan Majalisar Wakilai
A yayin haka ne Monica ta karbi sunan Maryam, ita kuwa Blessing ta koma Khadija, sai kuma 'yar kankanuwar su mai sunan Nancy ta sauya zuwa ga Hafsa.
Shugaban Majalisar Malamai reshen kauyen Tilden Fulani, Mallam Abdullahi Adam tare da tawagar wasu mallumma na kauyen ne suka jagorancin bayar da kalmar shahada ga wannan mata.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng