Matasan Filato sun rubuta wa Buhari wasika akan hare haren makiyayan Fulani

Matasan Filato sun rubuta wa Buhari wasika akan hare haren makiyayan Fulani

-Matasan Filato sun koka da hare-haren makiyaya a jihar su

- Sunyi kira da shugaban kasa yaba jihar Filato kulawa ta musamman

- Shugaban kungiyar matasan ya ce sama da mutane 100 sun rasa rayukan su a harin da makiyaya suka kai kwanannan

Wasu matasa a Filato sun yi kira da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya cecei jihar su daga hare-haren makiyayan Fulani.

A wata budaddiyar wasika da matasan suka rubuta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sun ce makiyaya sun kashe sama da mutane 100 a jihar tare da jikkata mutane da dayawa.

A harin da makiyaya suka kai masarautar Irigwe dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato, sun kona gidajen mutane da dama, da yin awon gaba da dukiyoyin su.

Matasan Filato sun rubuta wa Buhari wasika akan hare haren makiyayan Fulani
Matasan Filato sun rubuta wa Buhari wasika akan hare haren makiyayan Fulani

Kungiyar matasan mai suna Plateau Youth G-17 Peace and Progressive Forum, dake karkshin jagorancin Dachung Bagos, yayi kira da shugaban kasa ya ba jihar Filato kulawa ta mussaman dan kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar.

KU KARANTA : Wike ya baranta daga fostocin da ya nuna yana neman mataimakin shugaban kasa a zaben 2019

Bagos yayi gargadi da cewa, rashin bin dokokin tsaro yasa rikicin ta kara barke wa a kananan hukumomin Bassa, Arewacin Jos, Barikin Ladi, Riyom da Bokkos.

Ya ce makiyayan sun ci mutuncin mutane, tare da kashe mata da kananan yara.

An kashe mutane 6 a harin da aka kai kauyan Ta’agbe a daren a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba, bayan haka an kashe mutane 29 da jikkata mutane da dama a harin da aka kara kai wa masarautar Nkiedonwhro, Irigwe dake karamar hukumar Bassa jihar Filato.

Duk da sojojin da aka tura kauyuka dan kare rayuka da dukiyoyi, ana cigaba da kashe mutane.

“Har Idan masu kai harin suna da zuciyar kashe jami’an tsaro, yaya al’amarin mu zai kasance kenan?.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng