Muhimman amfani guda 5 da ɗanyen ƙwai ke da shi ga fuskar dan Adam
Masana sun bayyana wasu kwararan amfani da danyen kwai ke da shi ga lafiyar dan Adam, musamman wajen gyaran fuska, tare da kare fuskar daga matsalar kuraje.
Jaridar Aminiya ta dauko wani rahoto da yayi nuni akan wasu daga cikin wadannan alfanu da kwai ke da su wajen magance kurajen fuska.
KU KARANTA; Shiriya daga Allah: Babban Fasto ya Musulunta, an koma yin Sallah a Cocinsa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito danyen kwaia nada amfani ga fuskar mutum kamar haka:
1- Ruwan kwai nada sinadarin gina jiki, da kuma sinadaran Bitamin
2- Ruwan kwai na rage tsufar fuska
3- Danyen kwai na kare fuska daga yawaitan fitar kuraje
4- Danyen kwai na kara ma fuska haske
5- Ruwan kai na rage kumburin idanu
Yadda ake hada ruwan kwai don samun bukata shine, za’a fara turara fuska da ruwan zafi, sa’annan abi da Rose water a shafe fuskar, kamar yadda majiyar mu ta ruwaito.
Daga nan sai a fasa kwai, a cire kwaiduwar, sai a kada farin ruwan kwan, har sai yayi kumfa, bayan nan sai a shafe fuska da wannan ruwan kwai, sai kuma a daure fuskar da takardar ‘Tissue’ a manna a fuskar, a kara samun takardar a sake mannawa a dukkanin fuskar.
Da zarar fuskar ta bushe a haka, sai wanke fuskar, sa’annan a shafe fuskar da kwaiduwar ita ma, sa’annan a wanke, idan an cigaba da wannan tsari, za’a samu biyan bukata.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
An rasa maganin cutar kyandar biri, kalla a Legit.ng TV
Asali: Legit.ng