Real Madrid, Zidane da kuma Ronaldo sun kafa muhimmin tarihi duk a wasa guda
Kungiyar kwallon kafar nan ta Real Madrid ta kafa tarihin da ba'ataba kafawa ba bayan da suka ci wasan su na 13 a jere a gasar La Liga bayan da suka doke kungiyar Getafe a wasan mako na 8 a ranar Asabar din da ta gabata.
Kungiyar ta Real Madrid dai dake buga wasan ta a kasar Sifen ta doke kungiyar Getafe ne da ci 2 - 1 inda kuma dan wasan su na gaba Karim Benzema ya zura kwallon farko kafin aje hutu rabin lokaci sannan kuma Cristiano Ronaldo ya jefa ta biyun ana daf da tashi wasan.
KU KARANTA: Har yanzu Shugaba Buhari bai shiga ofishin sa ba
Legit.ng dai ta samu cewa da wannan sakamakon ne kungiyar ta Real ta doke tarihin cin wasa a waje 12 da kungiyar Barcelona ta taba kafa a karkashin jagorancin kocin su Pep Guardiola a shekara ta 2009/10 da kuma 2010/11.
Wannan dai ba shine karon farko ba da kungiyar ta Real Madrid karkashin jagorancin kocin ta Zinedane Zidane ke doke tarihin da kungiyar Barcelona ta kafa ba tun bayan da anshi ragamar kungiyar kimanin shekaru biyu da suka gabata.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng