Zan cigaba da cin abinci da harkar barkwanci, ko da Buhari ya sauka daga mulki – Mc Tagwaye
Shahararren mai sana’ar barkwancin nan, mai suna Mc Tagwaye ya bayyana asalin kabilarsa, inda yace shi dan kabilar Ibo ne, kuma sunansa na gaskiya Obinna Simon.
Shi dai Mc Tagwaye ya shahara ne wajen kwaikwayon shugaban kasa Muhammadu Buhari, tare da tsananin kama da yayi da Buharin, wanda hakan ne yayi silar dagawarsa a sana’ar barkwanci, amma jaridar Premium Times ta ruwaito shi yana fadin cewa ko da shugaban kasa Buhari ya sauka, ba zai daina cin abinci a sana’ar tasa ba.
KU KARANTA: Malamai sun bada amsa game da halasci ko haramcin aiki a kamfanin sigari
“Buhari ya riga ya kafu a siyasar Duniya, don haka ko baya nan, zan iya cigaba da kwaikwayonsa har sama da shekaru 100” kamar yadda ya shaida ma gidan talabijin na Hip Tv.
Simon ya shaida ma majiyar Legit.ng cewar haihuwarsa da aka yi da kuma girma da yayi a garin Katsina ne ya bashi damar kwaikwayan shugaban kasa Buhari, kuma shi dadadden masoyin Buhari ne.
Simon yace bai fara kwaikwayon Buhari ba sai bayan daya kalli wani hira da jaridr Sahara Reporters ta yi da shi a shekarar 2011,tun daga nan ne fa kakarsa ta yanke saka.
“Ka san Buhari janar ne a Soja, baya dariya, amma ranar da muka hadu a wani taro a Katsina, da na fara barkwanci har sai da Buhari yayi dariya. Bayan na gama wasa na, sai na tafi wajensa da nufin mu dauki hoto, duk da jami’an tsaron dake gadinsa, caraf ya mike, muka gaisa, sa’annan muka dauki hoto tare.
“Bayan na wuce sai wani gwamna ya fada masa ai mu yan biyu ne, sai Buhari ya sa aka gayyaci tagwayena, shima suka dauki hoto da shi.” Inji shi
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Source: Legit.ng TV
Asali: Legit.ng