Man Kadanya: Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 3 da wani kamfani daga Malaysia

Man Kadanya: Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 3 da wani kamfani daga Malaysia

Kadanya dai itaciya ce mai albarka, bayan ta bada inuwa, ta kuma bada kadanya a ci, sannan ta bada mai daga gare ta, wato man kade, yanzu kuma, an gano cewa man nata za'a iya aya dashi makamashi, kamar dai diesel.

Idan aka tace man kadanya, aka sarrafa shi, zai samar da mai maras mugunyar hayaki, da za'a iya konawa ko a jannareta, ko a girki, ko ma a gingimari. Wannan mai na kadanya dai ana tatsarsa daga kadanya wadda ko'ina tana nan birjik a arewacin kasar nan.

Man Kadanya: Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 3 da wani kamfani daga Malaysia
Man Kadanya: Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 3 da wani kamfani daga Malaysia

A yanzu, gwamnain Tarayya ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da wani kamfani na Malaysiya, mai suna Bionas Agropolitants Technology Corridor Development, ta dala biliyan biyu da rabi, wato kusan tiriliyan daya na nairori. Inda za'a ara noma itaciyar a shirin kare hamada daga kwaranyowa.

A cikin shirin, za'a ciri 'ya'yan itaciyar ne, a kuma sanya su inji, a tsotso man kade, sai a kai kasar ta Malaysiya domin sarrafawa zuwa man fetur, ko diezel, domin amfani ga motoci da sayarwa domin riba.

DUBA WANNAN: Sanata Abaribe yace sun shiga uku bayan karbo belin Nnamdi Kanu

Wannan dai a cewar gwamnati, zai karo ayyukan yi, ya kuma karo wa gwamnati kudaden shiga, da ma rage dogaro da danyen man fetur, da duk siyasar da ta dabaibaye hako shi. Da turanci dai ana kiran kadanya/kade da Jatropha Curcas.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng