Samari da 'yan mata a Kano na kwankwadar kalaben maganin mura miliyan 3 kullum
Kimanin kwalebanin magungunan mura masu sa maye dake dauke da sinadarin Codeine ne matasa ke kwankwadewa a kullum rana a jihohin Kano da Jigawa kamar dai yadda majalisar dattijai tayi ikirari.
Wannan alkaluma dai an samesu ne a cikin wani kudurin da dan majalisar na dattijai mai wakiltar jihar Borno mai suna Sanata Baba Kaka Bashir Garbai tare da wasu sauran yan majalisar su 37 da suka gabatar a zauren.
KU KARANTA: Ilimi ya shiga mawuyacin hali a jihar Kaduna
Legit.ng ta samu har ila yau cewa kudurin dai da yake so hukumomi suyi duba ga yadda ake safara tare da tu'ammali da magungunan mura din masu sa maye barkatai musamman ma dai a yankunan arewa maso yammacin kasar nan.
Sauran wadanda suka yi tsokaci akan kudurin sun hada da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Sanata Jubrin Barau inda suka bukaci majalisar da ta bullo da wani daftarin doka da zai kawo karshen wannan bala'in da a cewar su zai iya yin mummunan lahani ga al'umma.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng