Daga wasan fatalwa, mutum biyar masu farautar mayu suka hallaka a kasar Malawi
Kai kace a nan Najeriya ne, tsoron aljannu da fatalwa ya ratsa mutanen kasar Malawi, a kudancin Afirka. Chamfe-chae sunyi wa kasashen bakar fata katutu, inda dama idan akwai rashin ilimi, jahilci kan mulki tunanin jama'a. Har su fara tsoron abubuwan da basu, suce akwai su.
Wasu samari da suka dauki doka a hannunsu, suke kiran kansu 'yan sintirin kama fatalwa, sun kashe a kalla mutane biyar a yankin Mulanje da Phalombe, a kudancin kasar ta Malawi, mai karancin arziki da ilimin boko.
Wadanda aka kashe din dai, mutane ne, amma wai ana zargin ko dai su mayu ne, ko aljannu ko fatalwa, saboda dai tsantsar jahilci da ya ratsa mutanen yankin na kudancin Afirka. Tuni dai tashe-tashen hankulan suka kori ma'aikatan majalisar dinkin duniya masu bada agajin ilimi da magunguna a yankin.
DUBA WANNAN: Sunki binne shi a makabartar musulmi saboda aradu ce ta kashe shi
Shugaba Mutharika dai yace wadannan labaru na matukar bashi haushi, inda ya yi alla-wadai da kashe-kashen na chamfi, ya kuma sanya dokar hana fita da dare har sai abin ya lafa. Ya kuma lashi takobin kamo wadannan 'yan sintiri masu farautar wai mayu da aljanu da fatalwi.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng