Kishi! Wata mata ta kashe mijin ta don zai kara aure
Yanzu haka dai iyalan wani mutum magidanci mai suna Danlami Abdullahi, da aka fi sani da suna Dan Hajiya, nacan suna zaman makomi a garin Kontogora na jihar Neja, a dalilin rasa ransa da yayi ta sanadiyyar matse masa azzakari da ake zargin matarsa ta aikata masa.
Bayanai sun nuna cewa an sami sabani ne a tsakanin rahorannin da muka samu daga majiyar mu dai sun bayyana cewa ma'auratan Danlami da kuma matar sa mai suna Rahanatu Abdullahi sun samu 'yar hatsaniya ne a sanadiyyar karin auren da ya ce zai yi.
KU KARANTA: Arewa zata yi matsaya kan sake fasalin kasa ranar Laraba
Legit.ng ta samu kuma dai cewa ma'auratan sun shafe fiye da shekaru 8 a tare yayin da kuma Allaha ya albarkace su da samun yaya 3 kafin mijin ya gamu da ajalin na sa.
Da aka tuntubi jami'an yan sanda sun bayyana rashin masaniyar sa game da lamarin inda suka tabbatar da cewa za su bincika sannan kuma su bayar da cikakken rahoto.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng