Yawan musulmai zai zarta na Kiristoci nan da shekara ta 2070 - Bincike

Yawan musulmai zai zarta na Kiristoci nan da shekara ta 2070 - Bincike

Wani sabon rahoton bincike da wata cibiyar binciken al'amuran yau da kullum ta duniya mai suna Pew Research Centre a turance ta fitar yayi ishara da cewa yawan mutane musulman duniya zai zarce na kiristoci kafin nan da shekarar 2070.

Haka ma dai rahoton da cibiyar binciken ta fitar ya kuma bayyana cewa addinin na Islama shine addini mafi amintuwa ga hukumomin gwamnatocin kasashe a duniya kamar dai yadda binciken na su ya tabbatar.

Yawan musulmai zai zarta na Kiristoci nan da shekara ta 2070 - Bincike
Yawan musulmai zai zarta na Kiristoci nan da shekara ta 2070 - Bincike

KU KARANTA: Dole a maida Juma'a ranar hutu - Inji MURIC

Legit.ng ta samu cewa a yayin binciken nasu cibiyar nazarin ta gano kuma cewa a halin yanzu akalla kasashen duniya 27 ne suka amince da addinin musulunci a hukumance sabanin kasashe 13 kacal da suka amince da addinin kiristanci ciki kuwa hadda kasar Birtaniya.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya mun kawo maku wani rahoto inda aka umurci musulman wani yanki a kasar China da su tattara kur'anan su su kaiwa hukumomin gwamnatin su ko kuma ayi masu ukuba, lamarin da ya gamu da suka daga jama'ar musulman duniya baki daya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng