Rayuwar Mata a yankin Arewa na cike da ƙalubale masu tarin yawa – Inji Rahama Sadau
Shahararriya yar wasan Hausan nan mai suna Rahama Sadau ta bayyana mawuyacin halin dake tattare da tabbatauwar burin yan matan Arewa masu bukatar zama wani abu a rayuwa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Rahama Sadau na fadin haka ne cikin wata hira da tayi da jaridar This Day, inda ta bayyana ra’ayinta game da batutuwa da dama da suka shafi rayuwarta.
KU KARANTA: Mai kan uwa da wabai: Ýan bindiga sun bindige mutane 10 a jihar Ribas
Idan ba’a manta ba dai a shekarar data gabata ne kungiyar yan wasan Hausa na Kannywood suka sallami Rahama Sadau daga harkar Fim gaba daya, biyo bayan wani bidiyon waka data fito a ciki.
MOPPAN ta zargi Rahama Sadau da bayyana dabi’ar da bata dace da addinin Musulunci da kuma al’adar Bahaushe ba a cikin wannan bidiyon data fito na wani mawaki mai suna ClassiQ.
Sai dai Rahama ta danganta nasarar data samu da kuma daukakar data samu ga wannan sallama da MOPPAN tayi mata, inda tace hakan ne ya sa ta samu wasu damanmaki a gida da wajen Najeriya.
Tsohuwar Jarumar Kannywood ta cigaba da fadin cewa zata cigaba da dagewa wajen kulawa tare da baiwa al’adarta da kuma tarbiyyarta fifiko kafin ta amince da shiga wani Fim, musamman a fina finan Turanci, Nollywood.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a baya ma an yi ma Rahama Sadau tayin shiga wani Fim na Turanci, inda aka bukaci ta kwaikwaiyi mata yan madigo a ciki, amma tayi watsi da wannan tayin saboda addinin Musulunci da kuma al’adar Hausa basu yar da hakan ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Wanenne gwaninka cikin shuwagabannin nan? kalla a Legit.ng TV
Asali: Legit.ng